Macron ya zargi abokiyar takararsa Le Pen da hulda da Putin
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi abokiyar takarar sa Marine Le Pen saboda mu’amala da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya musanta cewar ya goyi bayan Rasha na mamayar Ukraine.
Wallafawa ranar:
Yayin ziyarar Brittany domin yakin neman zabe, Macron ya shaidawa manema labarai da su daina sanya ido akan sa saboda alaka da Putin, inda yake cewa ya dace su sanya ido akan sauran Yan takaran.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ko da ya ke Macron bai furta sunan Le Pen ba, yana nuni ne gare ta saboda yadda Putin ya karbe ta a shekarar 2017.
Le Pen dai ta nesanta kanta da shugaba Putin bayan da ya mamaye Ukraine, tana mai cewa ya sauya daga mutumin da ta hadu da shi a shekarar 2017.
Macron ya ci gaba da dasawa da Putin ko bayan mamayar Ukraine da kasarsa ta yi a 24 ga watan Fabrairu, amma fa ya ce ya yi haka ne bisa bukatar hakan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya mika masa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu