Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Macron zai nemi wa'adi na biyu a zaben Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar kan wa'adi na biyu a zabe mai zuwa, wanda ake kyautata zaton cewar yakin Rasha a Ukraine ka iya mamaye yakin neman zaben na watan Afrilu, koda yake  batun ka iya zama tagomashi ga shugaban.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Ludovic Marin
Talla

Macron ya bayyana aniyar zama shugaban kasar Faransa na farko da aka sake zabensa cikin shekaru 20 ne cikin wata wasika da ya aikewa Faransawa, wadda wasu shafukan kafafen watsa labarai da dama suka wallafa ta yanar gizo.

An dai shafe tsawon lokaci ana dakon shelar ta shugaba Macron, wadda fuskanci jinkiri lokuta da dama a baya saboda rikicin gabashin Turai tsakanin Rasha da Ukraine, wanda shugaban na Faransa ke kan gaba wajen kokarin sasanta shi.

Cikin sakon nasa, Macron ya amince cewa zaben bana ba zai kasance kamar wanda aka saba yi ba, saboda yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a baya bayan nan dai ya nuna cewar, Emmanuel Macron ne kan gaba a a tsakanin ‘yan takarar da za su fafata a zaben shugabancin Faransa da za a yi a ranakun 10 da kuma 24 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.