Isa ga babban shafi

Zan jagoranci samar da dokar kada kuri'ar yanke kauna kan shugaba Macron - Le Pen

Guda daga cikin jagororin adawar Faransa Marie Le Pen ta sanar da shirin gabatar da kudurin dokar kada kuri’ar yanke kauna kan Shugaban kasar Emmanuel Macron game da shirin sa na yunkurin amfani da karfi wajen tabbatar da sabuwar dokar tsarin Fansho. 

Marine Le Pen, daya daga cikin jagororin 'yan adawa a Faransa.
Marine Le Pen, daya daga cikin jagororin 'yan adawa a Faransa. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

A cewar ta, wannan shirin da Macron ke yi abin kunya ne gare shi dama gwamnatinsa baki daya, kasan cewar sa jagoran al’umma don haka bai kamata ya dauki matakin da mutane ke adawa da shi ba. 

A wani jawabi da ta wallafa a shafin ta na Twitter, Marie Le Pen ta ce matukar Faransa na ikirarin kasace da ke tafiya kan doron dimukaradiyya, ya kamata Emmanuel Macron ya saurari koken jama’a. 

Tun bayan da Emmanuel Macron ya sanar da shirinsa na mayar da sabon tsarin fansho zuwa doka, ‘yan kasar ke ta faman zanga-zanga da nuna adawa da wannan kuduri. 

Sama da watanni bayan haka kuma shugaba Emmanuel Macron ya bukaci yan majalisa su sahalewa kudurin nasa ya zama doka, sai dai ya gamu da tutsun masu adawa a majalisar, dalilin da yasa shi yanke hukuncin amfani da karfin ikon da ya ke da shi a bisa doka wajen tabbatar da sabon tsrain. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.