Juncker ya bukaci kasashen Turai su daina kyamar ‘yan ci-rani
Shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya bukaci gwamnatocin Turai su dai na kyamar ‘Yan ci-rani da ke ci gaba da tururuwa domin shiga kasashen.
Wallafawa ranar:
Juncker ya ce kasashen na da rawar da zasu taka wajen magance kwararar ‘Yan ci-ranin maimakon korarsu daga kasashen.
Yawancin ‘Yan ci-ranin dai ‘yan asalin Syria ne mai fama da rikici da kuma ‘yan Eritrea da ke ci gaba da kwarara ta mashigin Italiya da Girka.
A watan Oktoba ne dai mambobin kasashen Tarayyar Turai suka amince da matakin rarraba ‘yan ci-ranin kimanin 32,000 a tsakaninsu, amma har yanzu wasu kasashen sun ki karbar ‘Yan ci-ranin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu