Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya

Faransa da Birtaniya sun dauki matakai akan ‘Yan ci-rani

Kasashen Faransa da Birtaniya, sun sanar da daukar sabbin matakai da za su yi amfani da su domin magance matsalar kwararar bakin haure wadanda yanzu haka daruruwansu ke neman tsallaka iyakar Faransa zuwa Birtaniya daga wani yanki mai suna Calais.

An tsaurara matakan tsaro domin dakile kwararan 'yan ci rani a yankin Calais.
An tsaurara matakan tsaro domin dakile kwararan 'yan ci rani a yankin Calais. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve da takwararsa na Birtaniya Teresa May, sun bayyana a wata sanarwar hadin-giwawa a jiya Lahadi cewa, kasashen biyu za su yi amfani da hanyoyin da suka dace domin mangance yadda yanzu haka daruruwan baki ke kokarin kutsa kai zuwa Birtaniya daga mashigin Calais da ke cikin Faransa.

Domin magance wannan matsala, gwamnatin Birtaniya ta sanar da ware yuro milyan 15 wadanda za a yi amfani da su wajen tsaurara matakan tsaro akan iyakar, kuma za a fitar da kudi miliyan 10 na kudade a wannan mako.

Gwamnatin Faransa za ta tura karin ‘yan sanda 550 zuwa yankin iyakar, domin kange bakin hauren da ke ci gaba da tururuwa zuwa yankin na Calais.

A cikin makon da ya gabata jami’an tsaron Faransa sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin bakin hauren a lokacin da suka yi kokarin hana tsallakawa, lamarin da shugaba Francois Hollande ya bayyana shi da cewa kasar ba za ta iya magance shi ba sai tare da taimakon Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.