An tsinto gawarwakin ‘yan ci-rani 12 a tekun Italiya
Kimanin Bakin Haure 12 aka tabbatar da mutuwarsu bayan kwale-kwalen da ke shake da ‘yan ci-rani ya nutse a tekun Mediterranean a lokacin da suke kokarin tallakawa zuwa Turai.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jami’an Italiya sun ce sun yi nasarar ceto bakin haure kimanin 500 a cikin kwale kwalen da ya nutse a teku.
Kwale-kwale da ke shake da bakin haure ya nutse ne a tekun Mediterranean duka mile 40 da arewacin Libya , kuma jami’an ruwan Italiya sun ce sun yi nasar kubutar da ‘yan ci-rani kimanin 500, yayin da aka tsamo gawarwakin mutane 12 a ruwa.
Jami’an Italiya sun ce a jiya Alhamis kawai kusan ‘yan ci-rani 400 aka ceto a teku, da wasu kuma da aka ceto a kusa da tsibitrin Lampedusa.
Zuwa yanzu ba a bayyana ko ‘yan wace kasa ba ne aka ceto daga tekun.
Dubun dubatar mutane ne ke ci gaba da kokarin zuwa ci-rani a Turai duk da hatsarin da ke tattare da yanayin balagurun a tekun Italiya da Girka.
Yawansin ‘yan ci-ranin na gujewa yake yake ne da matsanancin rayuwa a kasashen Afrika da gabas ta tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu