Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta soki Birtaniya akan bakin haure

Kasar Jamus ta caccaki Birtaniya akan kaucewa shirin kasasshen Turai na karbar bakin haure da suka gujewa kasashensu sakamakon matsalar talauci da yake-yake.

Bakin haure a kwance a Kwangirin Jirgi da ke kusa da iyakar kasashen Italiaya da Faransa
Bakin haure a kwance a Kwangirin Jirgi da ke kusa da iyakar kasashen Italiaya da Faransa Reuters/Eric Gaillard
Talla

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabreil ya soki Birtaniyya na kaucewa tsarin taimaka wa bakin-hauren wadanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen arewacin Afrika da kuma yankin gabas ta tsakiya kuma sun gujewa matsalar talauci ne da yake yake.

A watan da ya gabata ne shugabannin kasashen Turai suka amince da bai wa Bakin-haure dubu sittin mafaka, sai dai kuma kasar Birataniya ta tsame kanta daga dokokin da tarayyar Turai ta gindaya a game da kan iyakokin kasashen.

Sasashen Ireland da Denmark sun bi sahun Birtaniya yayin da shugabannin Tarayyar Turai suka aminmce da yi wa kasashen Hungary da Bulgaria uzuri na rashin karban bakin.

A lokacin wani taron muhawara, inda aka yi tamboyi tare da bada amsoshi, Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya kare manufar kasar ta bai wa bakin haure mafaka inda ya kara da cewa, yana kyautata zatan al’ummar Jamus na taka rawar gani a wannan lokacin fiye da sauran kasashe da dama dangane da karbar bakin haure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.