Isa ga babban shafi
MDD-Africa

Bakin haure dubu 137 ne suka nemi shiga Turai a bana

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin Bakin haure dubu137 ne suka nemi tsallaka tekun Méditerranéen zuwa Turai a bana, yawancinsu suna kokarin kaurace wa yake-yake ne a kasashensu da kuncin rayuwa musamman a kasashen Afrika da yankin Asiya. 

Wasu daga cikin Bakin haure dake kokrin tsallaka wa turai
Wasu daga cikin Bakin haure dake kokrin tsallaka wa turai REUTERS/Stringer TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Hukular kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce matsalar kwararar bakin haure babbar matsalar ce da ba a taba gani ba.

Rahoton da hukumar ta fitar ta ce, cikin mutane dubu 137 da suka nemi shiga tekun, kimanin dubu 75 ne daga cikin su suka isa Turai ya yin da saura suka mutu.

Hukumar ta MDD ta ce akwai alamun kuma matsalar za ta ci gaba da karuwa, idan ba dauki matakai ba akan masu fataucin mutane su tsallaka da su zuwa Turai.

‘yan kasashen Syria da Eritrea da Somalia da Najeriya da Iraqi da Sudan ne suka fi yawan neman tsallaka wa zuwa Turai a cewar Rahoton.

Batun bakin haure dai a yanzu, ya zama wani babban kalubale ga kasashen Turai inda ake samun sabani tsakanin kasashen akan matakan da ya dauka domin shawo kan matsalar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.