Isa ga babban shafi
Italiya

Bakin haure na fuskantar kyama a Kasar Italiya

A Kasar Italiya, bakin haure dake neman mafaka a wajen birnin Rome na bukatar jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma domin kare su daga masu zanga zangar adawar karbarsu yayin da a arewacin Kasar wasu ke rusa gidaje domin hana bakin hauren samun wajen rabawa. 

Bakin haure kwance a tashar jirgin Kasa na Ventimiglia dake kusa da iyakan Italiya da Faransa
Bakin haure kwance a tashar jirgin Kasa na Ventimiglia dake kusa da iyakan Italiya da Faransa Reuters/Eric Gaillard
Talla

Italiya dai ta yi fice wajan karban bakin haure, kuma ta na ci gaba da karban bakin dake kwararowa kasar daga yankunan Afrika da gabas ta tsakiya.

Firai ministan Kasar Matteo Renzi na fuskantar matsin lamba na ya hana kwararar bakin yayin da gwamanatinsa ke ci gaba da kwantar da hankulan jama’a.
Sama da bakin haure dubu 85 ne suka shiga Italiya a wanna shekarar kawai.

A bangare guda, Kimanin bakin haure 40 ne suka rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin tsallkawa Turai, bayan kwale kwalen daya kwaso su ya nitse dasu a gabar ruwan Kasar Libya a ranar Alhamis.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.