Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

Ficewar Girka daga Kasashen Turai babbar barazana ce ga tsaron nahiyar

Manazarta sun ce ficewar Girka daga kasashe masu amfani da kudin Euro babbar barazana ce ga tsaron kasahen Turai.

Firai ministan Girka Alexis Tsipras yana gabatar da jawabi gaban Majalisar dokokinTarayyar Turai
Firai ministan Girka Alexis Tsipras yana gabatar da jawabi gaban Majalisar dokokinTarayyar Turai REUTERS/Vincent Kessler
Talla

lura da rawar da Girka ke takawa wajan samar da tsaro a kasashen Turai, da kuma cewa ta kasar ne bakin haure suka fi yin tururuwa shiga nahiyar Turai, manazartan sun ce ficewar Girkan zai fi zama babban tashin hankali ga nahiyar fiye da matsalar tattalinn arziki da nahiyar kan iya tsintar kanta a ciki, matukar rikicin bashin Girka ya yi kamari.

A cewar manazaartan ya kamata a fara lura da yawan bakin haure dake ci gaba da kokarin tsallka wa Turai yayin da rahotanni suka bayyana cewa a yan kwanakin nan, Girkan ta fi Italiya samun kwarar bakin haure, inda akalla yan cira dubu 48 ne suka shiga Kasar ta barauniyar hanya daga watan Janairu zuwa Mayu na wannan shekerar.

Manazartan sun kara da cewa matukar Girka ta ci gaba da samun matsala to lallai ba zata samu karfin gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyarta yadda ya kamata ba.

Yanzu dai an zura idanu ko hukumomin kasar ta Girka za su cimma yarjejeniyar karshe a wannan makon na ceto tatttalin arzikin kasar daga tabarbarewa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.