Wani Dattijo ya tallafawa Girka da kudadensa na Fansho
Wani Dattijo mai shekaru 88 a duniya a Cyprus ya aika wa Firaministan Girka Alexis Tsipras da kudadensa na Fansho kimanin yuro 506 a matsayin gudunmuwarsa ga kasar da ke fama da dinbin bashi.
Wallafawa ranar:
Dattijon ya taimakawa Girka ne da kudadenasa na Fansho domin biyan bashin da ake bin ta.
Dattijon da ake kira Onoufrios Michaelides ya fadi a cikin wasikar da ya aika zuwa Girka cewa ya yi haka ne saboda gamsuwa da matakan da Firaministan ke dauka na kare martabar Girka da al’ummarta.
Dattijon ya bukaci Tsipiras ya ci gaba da kare martabar kasarsa daga manyan kasashe ‘yan jari-hujja.
Dattijon wanda ke sayar da kayan wuta a shagonsa da ke birnin Limassol ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa ya yanke shawarar taimakawa kasar Girka ne saboda tausayin mutanen kasar da ya gani a Telebijin suna dogon layi wajen cirar kudi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu