Turai ta ba Girka wa’adi zuwa Alhamis
Shugabannin Kungiyar kasashen da ke amfani da kudin yuro sun ba kasar Girka wa’adi zuwa gobe alhamis domin ta gabatar da sabon shirin biyan bashinta wanda shugabanin za su yi nazari akai ranar lahadi don kaucewa kasar ficewa daga kungiyar.
Wallafawa ranar:
Shugaban Majalisar kungiyar Donald Tusk ya ce wannan shi ne mataki na karshe da za su ba kungiyar.
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bukaci hadin kai don warware matsalar Girka.
Kasashen na Turai sun jira Girka ne ta gabatar da sabbin tsare tsarenta a ranar Talata bayan al’ummar Girka sun kada kuri’ar kin amincewa da bukatun ma su bin kasar Bashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu