Isa ga babban shafi
Najeriya-Turai

Najeriya ta kulla yarjejeniya da Turai kan ‘Yan ci-rani

Najeriya da Kungiyar Tarayyar Turai sun sanya hannu kan wata yarjejeniya dangane da yadda za a magance matsalar kwararar bakin haure daga Najeriya zuwa Turai. Jakadan kungiyar Tarayyar Turai a Najeriya da kasashen yammacin Afirka Michel Arrion shi ne ya sanar da kulla wannan yarjejeniya mai kunshe da manyan manufofi guda hudu.

Bakin-haure da ke kwarara zuwa Turai
Bakin-haure da ke kwarara zuwa Turai REUTERS/Jean-Pierre Amet
Talla

Wasu daga cikin manufofin yarjejeniyar sun hada da yaki da matsalar Bakin Haure domin kasantuwarta haramtacciya, lura da yadda wasu ke amfani da ita a matsayin sana’a ta hanyar safarar jama’a daga Afirka zuwa Turai.

Batun kare hakkin mutanen da ake tsarawa da nufin shigar da su Nahiyar Turai, wanda shi ma jigo ne daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta tanada, kuma dole ne a dauki matakan murkushe masu aikata hakan a cewar Mista Arrion.

Sai dai wani sashe na daftarin yarjejeniyar, ya ce ya zama wajibi a kare hakkin masu neman mafakar siyasa da kuma sauran mutanen da suka tsinci kansu a cikin hali na gudun hijira sakamakon yake-yake da kuma sauran bala’o’in rayuwa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ke tabbatar da mutuwar mutane akalla 30 wadanda aka tsinci gawarwakinsu a cikin dajin Hamada na jihar Agadez da ke arewacin jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.