Kasuwanci
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
CISLAC ta horas da 'yan majalisun Najeriya kan muhimmacin haraji ga kasa
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan jan hankali da kungiyoyi irinsu CISLAC ke yi a Najeriya, wajen ganin gwamnati ta maida hankali kan gibi da ake samu a fannin tara haraji domin samun kudaden shiga.18/10/202309:56 -
Yadda Proparco ta ba da gudummuwa ga tattalin arzikin Najeriya cikin shekaru 15
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan bukin cika shekaru 15 cibiyar bada lamuni da raya kasashe ta kasar Faransa Proparco ta yi ta na gudanar da ayyukanta a Najeriya, inda ta zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a kasar cikin shekarun. Shirin zai mayar da hankali ne kan yadda ayyukan cibiyar ke bayar da gudunmawa ga fannonin daban-daban na ci gaban tattalin arzikin Najeriya.17/10/202309:36 -
Jiragen ƙasa sun fara jigilar kayayyaki daga Legas zuwa Ibadan
Shirin 'Kasuw akai Miki Dole na wannan makon ya tattauna ne kan yunkurin gwamnatin Najeriya na rage cunkuso a tashar jiragen ruwan ta Apapa da ke birnin Legas, wajen kaddamar da aikin soma kwashe kwantenoni daga tashar zuwa Ibadan da jirgin kasa na zamani.20/09/202310:21 -
Yadda kwanaki 100 na gwamnatin Tinubu ya riski ƴan Najeriya
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan mastin halin rayuwa da 'yan Najeriya suka shiga kwanaki 100 bayan kafa gwamnati.13/09/202310:19 -
Matsunta a Kamaru sun bukaci dage haramcin kamun kifi a Lagdo
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako, ya leka ne jamhuriyar Kamaru, inda matsunta da ‘yan kasuwa suka bukaci dage dabi’ar gwamnati kan dokar haramta kamun kifi na tsawon watanni uku - uku da ake yi a duk shekara, wanda ya kai ga gudanar da zanga-zanga a garin Lagdo dake arewacin kasar.06/09/202310:07 -
Tasirin tattalin arzikin shigar sabbin kasashe kungiyar BRICS
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako ya maida hankali ne kan taron Kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa wadanda suka kunshi Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu, wanda aka kafa ta domin kalubalantar kaifin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, wadda ta amince da shigar da sabbin kasashe shida cikinta amatsayin mambobi, wato Saudiyya da Iran da Habasha da Masar da Argentina sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.02/09/202310:15 -
Janye tallafin mai: Ta yaya tallafin gwamnatin Najeriya zai kai ga marasa galihu?
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya yada zango ne tarayyar Najeriya, inda Gwamnatin kasar ta ware kusan Naira biliyan 200, wanda ta rabawa jihohi 36 na kasar da birnnin tarayya Abuja da kuma motocin shinkafa, domin ragewa talakawa radadin da janye tallafin man fetur ya jefasu ciki. Ta yaya wannan tallafi zai kai ga marasa galihu, wadanda akayi dominsu? Abin da Shirin zai maida hankali akai kenan23/08/202310:15 -
Farashin kayan abinci ya yi tashin goron zabi a duniya
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole na wannan makon ya yi nazari ne kan yadda ake ci gaba da samun hau-hawan farashin kayayyakin abinci a kasashen duniya musamman nahiyar Afrika.16/08/202310:49 -
Takunkuman ECOWAS da UMOA sun fara tasiri kan al'ummar Nijar
Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jamhuriyar Nijar, inda ya duba halin matsin tattalin arziki da al’umma suka shiga sakamakon matakan kungiyar CEDEAO da UMOA na kakabawa kasar takunkumai saboda juyin mulki da sojoji su ka yi.10/08/202310:38 -
Janye tallafin man fetur ya jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali
Shirin 'Kasuwa A Kai Miki Dole' ya yi nazari ne kan tasirin janye tallafin man fetur a kan tataalin arzikin Najeriya, da irin halin da 'yan kasar suka sshiga tun bayan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki wannan mataki. Daya daga cikin bangaarorin da wannan mataki na gwamnatin Najeriya ya shafa shine bangaren harkokin sufuri, ganin yadda farashin shiga abin hawa ya tashi. A wasu sassan kasar wasu masu motoci sun sayar da ababen hawansu inda suka maye gurbinsu da babura ko kekuna.02/08/202310:32 -
Tasirin sabon matakin gwamnatin Najeriya kan kudaden waje
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmad Abba ya yi dubi ne kan tasirin matakan da gwamnatin Najeriya ta fara dauka na daidaita tattalin arzikin kasar wadda ta fara da baiwa bankuna damar yin hada hadar kasuwancin kudaden waje a farashin da suke so tare da janye kayyade adadin kudin waje da za’a yi cirewa kowace rana.21/06/202310:08 -
Halin da ake ciki bayan janye tallafin man fetur a Najeriya
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan batun janye tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin Najeriya ta yi, matakin da ya haddasa hauhawar farashin man zuwa fiye da ninki biyu kan kowacce lita guda.07/06/202309:54 -
An samar da masana'antar sarrrafa albasa a jihar Sokoto
Shirin Kasuwa akai miki Dole tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan noman albasa da tafarnuwa a jihar Sokoto ta arewacin Najeriya, jihar da ke matsayin kan gaba wajen noman albasar da tafarnuwa a kasar.31/05/202309:55 -
Najeriya - An kaddamar da Matatar man Dangote mafi girma a duniya
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne kan kaddamar da katafariyar matatar Man Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote a anguwar Lekki dake birnin Legas a kuduncin Najeriya.24/05/202310:22 -
Al'ummar Najeriya na ganin tsananin tsadar tumatur musamman a yanki kudanci
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya yi duba kan tsananin tsadar tumatir da ake gani a sassan Najeriya musamman yankin kudancin kasar wanda ya dogara da yankin arewaci gabanin samun kayan gwari inda rahotanni ke cewa farashin kwandon tumatur ya ninka fiye da sau 3 na farashin da aka saba sayen shi a baya.17/05/202309:47
Kasuwanci
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.