Isa ga babban shafi
Kasuwanci

CISLAC ta horas da 'yan majalisun Najeriya kan muhimmacin haraji ga kasa

Wallafawa ranar:

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan jan hankali da kungiyoyi irinsu CISLAC ke yi a Najeriya, wajen ganin gwamnati ta maida hankali kan gibi da ake samu a fannin tara haraji domin samun kudaden shiga.

Logon kungiyar farar hula ta CISLAC a Najeriya
Logon kungiyar farar hula ta CISLAC a Najeriya © CISLAC
Talla

Masana sun yi ittifakin cewar Najeriya na da dimbin arzikin da bai kamata ace sai ta ciyo bashin kudade kafin biyan bukatun ta ba, amma sakaci da kuma cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu ke mayar da ita baya.

Wannan yasa kungiyar CISLAC mai zaman kanta da ke sa ido kan ayyukan majalisar dokoki da kuma yaki da rashawa, da hadin guiwan cibiyar horar da ‘yan majalisun dokoki da demokuradiyya, suka shirya taro don horarwa da nunawa ‘yan majalisu rawar da za su taka wajen yin dokoki da saka ido a hanyoyin samar da haraji ga kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.