Isa ga babban shafi

Kotu a Jamhuriyar Nijar ta wanke janar Souleymane daga zargin yunkurin juyin mulki

A jiya Talata kotu a Jamhuriyar ya yi umurnin a saki Janar Souleymane Salou, wani tsohon babban hafsan sojin kasar, wanda aka yanke wa hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru 15 a shekarar 2018 sakamakon samun sa da hannu a wani yunkurin juyin mulki da aka yi a shekarar 2015. 

Jagoran gwamnatin sojin Nijar Janar Tchiani
Jagoran gwamnatin sojin Nijar Janar Tchiani AP
Talla

Wata majiya ta kusa da Janar din ta shaida wa kamfanin dillancin Labaran Faransa cewa an yi zaman sauraron daukaka kara da ya yi, kuma alkalin kotun ya bada umurnin a sake shi. 

Zalika wata majiya ta kusa da gwamnaatin sojin da ke mulkin Nijar ta tabbatar da wannan al’amari na sakin Janar din mai shekaru 70. 

Janar Souleymane Salou, wanda hafsa sojin sama ne, yana cikin sojojin da suka kifar da gwamnatin  Mamadou Tandja a shekarar 2010. 

Tuni dai sojojin suka fara shan chachaka, kan wannan hukunci, inda ake ganin sun yi biyayya gare shi ne kawai saboda kasancewar sa soja, la’akari da yadda suka saba yin biris da hukunce-hukunce kotu ko kuma umarnin a saki wasu mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.