Kotu ta tabbatar da Bazoum a matsayin shugaban Nijar
Kotun Fasalta Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da Bazoum Mohamed a matsayin sabon shugaban kasar wanda ya samu sama da kashi 55 na kuri’un da aka kada a zagaye na biyu na zaben watan jiya.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa bayan ‘yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben suna zargin an yi musu magudi, lamarin da ya haddasa kwarya-kwaryar tashin hankali har aka samu asarar rayukan mutane biyu a babban birnin Yamai.
Yanzu haka kotun ta ayyana cewa, daga ranar 2 ga watan Afrilun mai zuwa, Bazoum na da ikon jagorantar kasar ta Nijar a tsawon shekaru biyar.
Bazoum wanda tsohon Ministan Cikin Gida ne zai gaji shugaba Mahamadou Issofou mai barin gado wanda ya shafe wa’adi biyu na shekaru biyar-biyar kana karagar mulki.
A karon farko kenan da wani zababben shugaba ke mika mulki ga wani zababben shugaban daban tun bayan da kasar ta samu ‘yancinta daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarar 1960.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu