Isa ga babban shafi
Nijar

Tsohon shugaban kasa ya jagoranci zanga-zanga a Nijar

Dubban 'Yan adawa ne suka gudanar da zanga zanga a Jamhuriyar Nijar domin nuna rashin amincewar su da dokar zaben kasar da kuma rashin gamsuwa da jagoran gwamnati mai ci.

Tsohon shugaban jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane, yayin wata zanga-zanga a birnin Yamai
Tsohon shugaban jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane, yayin wata zanga-zanga a birnin Yamai AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

Tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane ya jagoranci zanga zangar inda suka yi ta zaga titinan birnin Yammai dauke da alluna na sukar gwamnatin dangane da abinda ya shafi matsalar tsaro da rashin jagoranci na gari.

Zanga zangar na zuwa ne mako guda bayan da Yan adawan suka janye daga cikin kwamitin dake sake nazarin dokokin zabe saboda rashin abincewa da batutuwa 4 da suka hada da haramtawa 'yan takara tsayawa zabe saboda zuwa gidan kaso na shekara guda.

Jam’iyyun adawan na ganin a yanzu ba wata tattaunawa da ta rage tsakaninsu da gwamnati, kamar yadda Sumana Sanda na jam’iyyar moden Lumana ya shaida mana.

"Ba cikin ji dadi ne nake gaya muku cewa zancen tataunawa tsakaninmu bai taso ba, komai ya toshe, dalilin da yasa yanzu muka ce hanya ce ma fi dacewa, mu fito a ji mu"

Shi kuma Bankono Maifada cewa, ya yi…

"Lokacin da suka so a yi abin da suke kira da sunan zaman tattaunawar yan siyasa, sai kuma suka lalata abin, saboda suna son su fito da kundin zaben da zai gyara su".

Ayar dokar kundin ta 8 ce, babbar matsala, in ji Jibrilla Bare na jam’iyyar RDP-Jama’a.

"To, matsalar ita ce, wannan ayar dokar ta 8 da ke cikin kundin zaben, wadda kuma manufarta shi ne kawai a hana ma mutum daya shiga zaben, ba daidai ba ne".

Shi kuma madugun yan adawa, tsohon shugaban Kasa Mammane Ousman na jam’iyyar Canji na ganin kawai Hamma Amadou ne karen farautar wannan kudirin doka.

"Abin ganewa a nan shi ne, a maido abin shekara daya, saboda kawai zai shafi dan uwanmu, Hama Amadou".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.