Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliyar ruwa ta rutsa da mutane akalla 50,000 a Nijar

Mutane 22 suka mutu sakamakon ambaliyar da aka samu a Jamhuriyar Nijar bayan ruwan sama mai karfi wanda ya shafi mutane kusan 50,000.

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 22 a Jamhuriyar Nijar.
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 22 a Jamhuriyar Nijar. RFIHAUSA/Awwal
Talla

Alkaluman da hukumomi suka bayar sun nuna cewa gidaje 3,000 suka rushe, yayin da eka sama da 4,000 na gonaki suka lalace.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI Ministan agajin gaggawa Lawan Magaji ya ce birnin Agadez na da wasu manyan duwatsu wadanda suke da akalla tsawon kilo mita 2 zuwa sama, wadanda daga nan ne idan aka samu saukar ruwan sama, ruwa ke gangarowa da karfin gaske lamarin da ke haddasa gagarumar ambaliyar ruwa ga duka karkarar da ya tarar.

01:08

Ministan agajin gaggawa na Jamhuriyar Nijar Lawan Magaji

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.