Manoma a Nijar na bukatar tallafin gaggawa don kafa kamfanin sarrafa albasa
Manoma da kuma masu sarrafa albasa a Jamhuriyar Nijar sun bukaci samun tallafin gwamnati domin fara aikin gina kamfanin sarrafa albasa na kasa da kasa a yankin Madawa da ke jihar Tawa wanda aka jima ana kokarin ganin samuwarsa.
Wallafawa ranar:
A cewar shugaban wannan shiri Mustapha Kadri Sarkin Abzin, lokaci na ci gaba da tafiya kuma matukar ba a yi wani abu ba to gwamnati da manoman kasar Senegal za su iya shiga gaban Nijar wajen yin fice a aikin na sarrafa albasa.
Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, sarkin Azbin, ya ce watanni hudu suka rage musu a dakon da ake wajen ganin gwamnatin Nijar ta bada kasonta na taimakon kudi don tabbatar da shirin gina kamfanin sarrafa albasa a yankin na Madawa karkashin tallafin wasu Faransawa. A cewarsa muddin wannan dama ta wuce su to fa zata koma ga kasar Senegal ko Burkina Faso.
NIGER-ONION-TRANSFORMATION-SCHEME-ABZIN-2017-04-12
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu