Malaman makaranta na yajin aiki a Nijar
Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar sun tsuduma a cikin yajin aikin gama gari a wasu manyan biranen kasar da suka hada da Yameh, Zinder, Maradi, Tahoua, domin neman ganin hukumomin kasar.
Wallafawa ranar:
Sai dai a wasu biranen kasar rahotanni sun ce ‘yan sanda sun tsare wasu shugabanin kungiyoyin malamai.
Malaman na yajin aikin ne saboda zargin taka hakkokin su.
Wani malami da ya nemi mu sakaya sunan sa ya tabbatar da gaskiyar halin da ake ciki yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI.
A bayanin nasa ya jaddada cewa malaman zasu cigaba da kasancewa kan bakansu na cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta saurari bukatunsu.
Malaman makaranta a Nijar na yajin aiki
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu