Isa ga babban shafi
Nijar- Mali

An kafa dokar ta baci a yankuna bakwai na Nijar

Kasar Nijar ta ayyana dokar ta baci a wasu yankunan yammacin kasar dake makwabtaka da kasar Mali sakamakon hare-haren ta'addanci da masu jihadi ke ta  kaiwa.

Shugaban Nijar  Mahamdou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamdou Issoufou REUTERS/Afolabi Sotunde/Files TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Wata sanarwan Gwamnati tun jiya Jumaa na cewa kafa dokar ta bacin ya shafi wurare  7 a yankunan Tilaberi da Tahoua.

Yanzu ke nan an karawa jami'an tsaro karfin guiwa da izinin binciken dukkan inda suke zargin akwai alamun rashin gaskiya.

A cewar sanarwan yawaitan hare-hare da ake kaiwa a yankunan na da hatsarin gaske ga mazauna yankunan.

Sauran sassan sun hada da Ouallam, Ayorou, Bankilare, Abala da Banbangou a yankin Tilaberi, sai kuma Tassara da Tilla a yankin Tahoua.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.