Isa ga babban shafi
Niger

'Yan Gudun hijiran Boko Haram da aka tsugunar a Nijar sun koka

Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijira dake sansannin da aka kebe a kasar Jamhuriyar Niger na ta korafe-korafe saboda yadda aka barsu babu kulawa daga Hukumomin bada agaji.

Al'ummar Jihar Borno da rikicin Boko Haram ya raba su da Muhallinsu
Al'ummar Jihar Borno da rikicin Boko Haram ya raba su da Muhallinsu AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Wasu da suka tattauna da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, AFP na cewa rayuwa a sansanonin babu dadi kokadan kuma Kungiyoyin dake bada agaji sam basu waiwaye su ba.

Akwai dai kimanin ‘yan gudun hijira akalla dubu shida a wasu sansanoni da aka ware kuma wasun su tun a bara suke cikin sansanonin.

Jami'in kula da Jin Kai Dauki na Majalisar Dunkin Duniya Stephen O'Brien wanda ya ziyarci sansanonin da aka jibge 'yan gudun hijira a Niger,  yayi gargadin cewa yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram ya yi muni domin ya haifar da munanan matsaloli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.