Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun gano babbar cibiyar da ‘Yan Boko Haram ke hada Bom

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta gano wata cibiya da kungiyar Boko Haram ke hada bama bamai da abubuwa masu fashewa a garin Ngala cikin Jihar Borno yankin arewa maso gabashi.

Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar cibiyar Boko Haram ta hada bama bamai
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar cibiyar Boko Haram ta hada bama bamai Nigerian Army
Talla

Kakakin rundunar Sojin Kanal Usman Kukasheka ya ce sojojinsu sun gano tunkunyar gas kusan guda 20 manya da kanana a cikin cibiyar hada abubuwan masu fashewa.

Sannan sojojin sun samu abubuwa da dama da ake amfani da su wajen hada bama bamai a cikin cibiyar ta yan Boko Haram a Ngala.

Kanal Usman ya ce sun gano inda ‘Yan Boko Haram ke hada bama baman ne daga bayanan sirrin da suka samu, sannan sun tarwatsa cibiyar tare da kashe ‘Yan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.