Kotun Ecowas ta bukaci kasar Nijar ta biya iyalen marigayi Ba'are diyya
Kotun kasashen yammacin Afirka Ecowas da ke birnin Abuja na tarayyar Najeriya, a yau juma’a ta bukaci hukumomi a jamhuriyar Nijar da su biya iyalan tsohon shugaban kasar Ibrahim Ba’are Mainasara diyya CFA milyan 435, sakamakon kisan da sojojin kasar suka yi masa a shekarar 1999.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Alkalan kotun da ta yanke wannan hukunci su biyar ne suka bukaci hukumomin kasar ta Nijar da su biya diyyar ta kwatankwanci Euro dubu 663, kimanin dalar Amurka dubu 750.
Kotun ta ce za a raba wa iyalan Ba'are da kudaden ne, inda matarsa za ta samu CFA milyan 75, kowanne daga cikin 'yayansa su biyar zai samu CFA milyan 50, yayin da za a raba sauran kudaden wato milyan 10 a tsakanin 'yan uwansa na jini su 11.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu