Isa ga babban shafi
Zaben-Nijar

Nijar ta bukaci kasashe duniya su tallafa wa zabubbukan shekara ta 2016 a kasar

Kasar Jamhuriyar Nijar ta bukaci kasashen duniya da su tallafa mata da miliyan 3 na Euro domin samun damar shirya zabubbukan 2016 a kasar, wadanda suka hada da na shugaban kasa da nay an majalisar dokoki a 2016, kamar yadda wani mamba a hukumar zaben kasar mai zaman kanta CENI ya sanar  

Le président Issoufou (D) et Hama Amadou, président à l'issue d'une cérémonie religieuse,à Niamey, le 7 avril 2011.
Le président Issoufou (D) et Hama Amadou, président à l'issue d'une cérémonie religieuse,à Niamey, le 7 avril 2011. AFP / BOUREIMA HAMA
Talla

Mataimakin shugaban hukumar zaben kasar ne, Lauya Kadri Umaru a cikin wata fira da tashar Talabijin a birnin Yamai babban birnin kasar, ya bayyana cewa, sun nemi aminan huldar kasar dake taimaka mata, da su taimaka da kashi 50 cikin 100/° na kasafin kudin da za a iya gudanar da zabubbukan kasar da su.

Ya kuma kara da cewa, yakuwar neman agajin an yi ta ne, a ranar alhamis da ta gabata a lokacin wani taro da ya hada hukumar zaben da jami’an diflomasiyar kasashen duniya dake zaune a kasar da kuma na kungiyoyi masu zaman kansu, tare da halartar wakilan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Niger

Daga cikin FCFA biliyan 38,809 miliyan 6 na Euro kenan, zaben shugabancin kasar zagaye na farko, da za a gudanar a 21 ga watan Fabrairun 2016, da za a hada da na yan majalisun dokoki ne, zai lakume FCFA biliyaN 12,777, a yayinda zagaye na 2 zai ci FCFA biliyan 6,458, kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar Ibrahim Bube ya sanar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.