Isa ga babban shafi
Nijar

An yi wa Gwamnati garambawul a Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou ya yi wa gwamnatinsa kwarya-kwaryan garambawul, inda ya raba wasu ma’aikatu zuwa biyu tare da shigo da wasu sabbin mutane a cikin gwmanatin.

Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou AFP Photo/Brendan Smilalowski
Talla

A karkashin wannan garambawul, duk da cewa Saidou Sidibe zai ci gaba da kasancewa ministan kudi da tattalin arziki, amma kuma an nada karamin minista mai suna Mohamed Boucha a wannan ma’aikata domin kula da tsara kasafin kudi.

Ma’aikatar fasali, da raya karkara, ita ma an raba ta gida biyu, inda aka bar minista mai ci Amadou Aboubacar Cisse domin rike sashen fasali, to amma an nada wata mai suna Madame Ibrahim Binta Fodi a matsayin wadda za ta tafiyar da sashen raya karkara.

To sai dai manazarta na kallon matakin da shugaba Issoufou Mahamadou ya dauka a ma’aikatar ta fasali a matsayin wanda ke kara fitowa fili da zargin sabani da ake cewa akwai tsakanin shugaban da Amadou Cisse, daya daga cikin wadanda suka mara masa baya har ya yi nasara a zaben shekara ta 2011.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.