Miliyoyin mutane za su bukaci agaji a Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 14 ne za su bukaci agaji a yankin arerwa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram nan da shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Majalisar ta kuma gargadi cewa, dubban kananan yara daga yankin na fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwa.
Babban jami’in majalisar a Najeriya, Peter Lundberg ya shaida wa taron manema labarai cewa, akalla mutane miliyan 26 ne matsalar Boko Haram za ta shafa a shekara mai zuwa, in da miliyan 14 daga cikin su za su bukaci agaji ga kasashen duniya.
Mr. Lundberg ya kara da cewa, a halin yanzu akwai kananan yara dubu 75 da za su iya rasa rayukansu nan da wasu watanni masu zuwa matukar aka gaza ba su taimakon da ya dace.
Rikicin Boko Haram dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 20 a cikin shekaru bakwai da suka gabata, tare da raba miliyoyi da gidajensu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu