Isa ga babban shafi

Fursunoni 118 sun tsere daga gidan yarin jihar Neja a Najeriya

Akalla fursunoni 118 suka tsere daga gidan yarin jihar Neja a Najeriya bayan da mamakon ruwan da aka samu a daren jiya Laraba wayewar yau Alhamis wanda ya rushe wani bangare na ginin kurkukun.

Wani gidan yari a Najeriya.
Wani gidan yari a Najeriya. © dailytrust
Talla

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya, Adamu Duza ya tabbatar da tserewa fursunonin daga jihar Neja ko da ya ke ya sanar da nasarar kamo 10 daga ciki, yayinda yanzu ake laluben 108.

A cewar Duza, yanzu haka suna aiki tare da wasu hukumomi don tabbatar da kamo ilahirin fursunonin da suka tsere don mayar da su kurkuku.

Kakakin na hukumar gidajen yarin ta Najeriya ya tabbatar da rushewar wani bangare na gidan yarin wanda ya ce shi ne ya baiwa masu laifin damar iya tserewa lokacin da ake tsaka da ruwan sama.

Wannan dai ba shi ne karon farko da fursunoni ke tserewa a jihar ta Neja ba, yayinda matsalar tserewar ta fursunoni da zarar sun samu kafa ke kokarin zama ruwan dare a sassan Najeriya.

A cewar Adamu Duza galibin gine-ginen an yi su ne tun a zamanin mulkin mallaka, kuma yanzu haka hukumar na aiki tukuru don ganin ta tabbatar da gyare-gyare ba kadai a gidan yarin na jihar Neja ba, har ma sauran gidajen yarin da ke bukatar gyare-gyare.

Wannan mataki dai na zuwa a dai dai lokacin da korafe-korafe suka yi yawa game da cunkoson gidajen yari a Najeriya inda masu ruwa da tsaki ke kira don ganin an rage cunkoson tare da gyaran gine-ginensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.