Isa ga babban shafi

Fursunoni 12 sun mutu a rikicin gidan yarin Ecuador

Bayanai daga kasar Equador na cewa wani rikici da ya tashi a tsakanin daurarrun gidan yarin Guayaquil ya i sanadin mutuwar mutane 12 a wannan Asabar, rikici mafi muni da aka gani a gidan yarin a baya-bayan. 

Shingen jami'an tsaro  a wajen gidan yarin Guayaquil na Ecuador inda ake yawan munanan arangama.
Shingen jami'an tsaro a wajen gidan yarin Guayaquil na Ecuador inda ake yawan munanan arangama. REUTERS - VICENTE GAIBOR DEL PINO
Talla

Tuni dai mahukuntan gidan yarin suka kaddamar da fara binciken musabbabin tashin rikicin, kamar yadda ya wallafa a shafin san a Twitter. 

Rahotanni sun ce rikicin ya tashi ne kwana guda bayan samun gawargwakin wasu daurarru 6, a rataye kuma har yanzu babu cikakken bayani kan ko rataye su aka yi ko kuma sune suka rataye kansu. 

Gidan yarin dai yayi kaurin suna wajen tashin rikci a tsakanin daurarru ta yadda har take kaiwa ga suna kisan junan su, la’akari da yadda ayyukan laifin da ake aikatawa a gidan yarin mai dauke da daurarru sama da 400. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.