Isa ga babban shafi
ECUADOR

Dutse da ya fado daga sararin samaniya ya fasa bututun mai a Ecuador

Kamfanin man kasar Ecuador yace kasar ta yi asarar ganga dubu shida da 300 daga rumbun adana man fetir din kasar, sakamakon yoyon mai da aka samu.

Yadda bashewar bututun mai ya mamaye gonaki a kasar Ecuador.
Yadda bashewar bututun mai ya mamaye gonaki a kasar Ecuador. Cristina Vega RHOR AFP/Archivos
Talla

A cewar kamfanin mai na kasar OCP lamarin ya janyowa kasar hasara mai yawa tun ranar Juma’a, sakamakon fadowar wani gungumemen dutse daga sararin samaniya kan babban butunun man da ke sada babban birnin kasar da yankin Mountainous.

Kamfanin mai na kasar ya ce ganga dubu 6 da dari uku na man da ya kwarare dai-dai yake da kaso 84 cikin dari na abinda kasar ta tanada don shirin ko ta kwana, abinda ke nufin yanzu watakila a iya shiga cikin halin karancin mai a kasar.

Da ya ke karin bayani shugaban kamfanin Jorge Vugdelija ta cikin sanarwar da ya fitar ya ce ana ci gaba da bincike don gano guraren da man ke fita da nufin gyarawa cikin gaggawa don rage yawan asarar da za’a yi.

Ya zuwa yanzu kusan fadin murabba’in kasa dubu 21 ne digar man ta mamaye, kuma fiye da rabi gonaki ne na nomar Coccoa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.