Isa ga babban shafi
Ecuador

Gwamnatin Ecuador ta bukaci ‘Yan Jarida biyan kudade

Wata Kotu a kaasr Ecuador, ta bukaci wasu ‘Yan Jaridu biyu biyan shugaban kasa, Rafael Correa, Dala miliyan daya kowannensu, saboda bata masa suna akan zargin da suka yi masa na bai wa Dan uwansa kwangilar makudan kudade.

Shugaban kasar Ecuardor Rafael Correa
Shugaban kasar Ecuardor Rafael Correa Reuters
Talla

‘Yan Jaridun biyu sun yi zargin ne a rahotan da suka wallafa, yayin da shugaban kasar yace, bashi da labarain cewar an bai wa Dan uwansa kwangilar Dala miliyan 167.

Bayan jin labarin ne shugaban ya soke kwangilar.

Shugaban kasar yace, bai gamsu da hukuncin kotun ba, saboda kudin tarar sun yi kadan, saboda haka zai daukaka kara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.