Isa ga babban shafi

Girgizar kasa ta kashe akalla mutane 15 a Ecuador da Peru

Akalla mutane 15 ne suka mutu wasu da dama suka jikkata a wata girgizar kasa da ta afku a kudancin Ecuador da Peru, wadda ta yi barna mai yawa, a jiya asabar.

Girgizar kasa ta yi barna a kasar Ecuado
Girgizar kasa ta yi barna a kasar Ecuado REUTERS/Guillermo Granja
Talla

Alkaluma daga cibiyar hasashe game da girgizar kasa ta Amurka USGS, girman girgizar kasar ya kai 6.8. Hukumomi a Ecuador sun ƙididdige shi a 6.5 kuma waɗanda ke cikin Peru a 6.7.

A Ecuador mutane 14 ne suka mutu a lardunan El Oro da Azuay da ke kudu maso yammacin kasar, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wata sanarwa daga fadar shugaban kasar

Taswirar kasar Peru
Taswirar kasar Peru Carte : RFI

A garin Tumbes na kasar Peru da ke kan iyaka da Ecuador an sanar da mutuwar wata yarinya ‘yar shekara hudu bayan da  bulo  ya fado mata a kai.

Girgizar kasar ta afku ne da karfe 12:12 na rana (5:12 na yamma agogon GMT), a zurfin kilomita 44, inda girgizar ta afku a garin Balao da ke da tazarar kilomita 140 kudu da babbar tashar jiragen ruwa ta Guayaquil ta Ecuador. Hakan ya haifar da barrazana a tsakanin mazauna garin da suka fito kan tituna. Gidaje sun rushe a garuruwa da dama da suka hada da Cuenca da ke lardin Azuay, daya daga cikin wadanda lamarin ya fi shafa.

A cibiyar tarihi ta Cuenca, 'yan jaridar AFP sun ga rugujewar gine-gine. Tituna da dama a wannan birni sun toshe sakamakon zaftarewar kasa da girgizar kasar ta haddasa.

Girgizar kasa a wani yanki na Ecuado
Girgizar kasa a wani yanki na Ecuado REUTERS - MARIA FERNANDA LANDIN

Hukumomin Ecuador sun ba da rahoton lalacewar gine-gine 360 ​​a cikin kasar. An samu zaftarewar kasa 22 a lardin Azuay.

Shugaban kasar Ecuador Guillermo Lasso ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, "Ina rokon a kwantar da hankula da kuma samun bayanai ta hanyar yanar gizo," Shugaban kasar Ecuador Guillermo Lasso ya isa lardin El Oro sannan vayan haka ya yi tataki zuwa  Cuenca don "ganewa idanun sa barnar da aka yi".

Brazil ta bayyana goyon bayanta ga kasashen biyu da abin ya shafa a ranar lahadin da ta gabata, kamar yadda Chili ta riga ta yi a jiya, tana mai cewa "a shirye ta ke ta ba da dukkan taimakon da ya dace ga hukumomi don daukar matakin gaggawa na jin kai".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.