Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Peru ta yi watsi da kiran shugabar kasar na shirya zabe karshen 2023

Shugabar kasar Peru Dina Boluarte a jiya Juma'a ta bukaci Majalisa da ta yi kokarin ganin an shirya zaben kasar a karshen shekarar 2023 wato Disamba a maimakon  watan Afrilun 2024 . 

Shugabar kasar Peru  Dina Boluarte a birnin  Lima  a wannan shekara ta 2023.
Shugabar kasar Peru Dina Boluarte a birnin Lima a wannan shekara ta 2023. AP - Martin Mejia
Talla

Shugabar ta bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da fuskantar zanga-zanga a cikin wannan kasa,al’amarin da ya hadasa mutuwar mutuwar mutane kusan 47. 

Kasar Peru ta fada cikin rikicin siyasa tare da zanga-zangar tun ranar 7 ga watan Disamba lokacin da aka kama tsohon shugaban kasar Pedro Castillo bayan yunkurin rusa majalisar dokokin kasar da kuma yin mulki ta hanyar doka. 

Masu neman shugabar kasar Boluarte ta yi murabus tare da kiran sabon zabe, su ne magoya bayan tsohon Shugaban kasar Castillo tare da  kafa shingaye kan manyan tituna, lamarin da ya haifar da karancin abinci, man fetur da sauran kayayyakin masarufi a kasar ta Kudancin Amurka. Gwamnatin ta ce nan ba da jimawa ba za ta tura ‘yan sanda da sojoji domin share shingayen. 

Majalisar dokokin kasar ta yi watsi da kiran da shugabar kasar ta yi na a gudanar da zaben da wuri. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.