Isa ga babban shafi

Gwamnatin Peru ta ayyana dokar ta-baci saboda rincabewar zanga-zanga

Gwamnatin kasar Peru ta sanya dokar ta baci a babban birnin kasar Lima da kuma wasu larduna 3 saboda tsanantar zanga-zangar kin jinin shugabar kasar Dina Boluarte, wadda  ta yi sanadin mutuwar mutane 42, a makon jiya kadai. 

Shugabar Peru, Dina Boluarte.
Shugabar Peru, Dina Boluarte. REUTERS - ANGELA PONCE
Talla

Dokar zata ci gaba da aiki har tsahon kwanaki 30, sannan kuma shugabar kasar ta baiwa sojoji izinin su kwarara cikin gari don tabbatar da doka da oda, yayin da ta kara da sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a da taron jama’a da sauran lamuran kai kawon mutane a yankunan. 

Tun bayan hambarar da shugaban kasar bayan wata mummunar zanga-zanga a kasar, Dina ta zama sabuwar shugaba, amma zanga-zangar ta ki karewa saboda yadda jama’ar kasar ke ganin babu wani banbanci tsakanin ta da shugaban da suka kora. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.