Isa ga babban shafi

Zanga-zangar adawa da sabuwar shugabar Peru ta rikide zuwa tarzoma

Akalla matasa biyu aka kashe yayin da wasu hudu suka jikkata a kasar Peru sakamakon zanga-zangar neman a gudanar da babban zabe a  kasar,  biyo bayan tsige  tsohon shugaban kasar Pedro Castillo.

Sabuwar shugabar Perú, Dina Boluarte.
Sabuwar shugabar Perú, Dina Boluarte. AP - Fernando Vergara
Talla

Tuni aka rantsar da shugaba Dina Boluarte a makon da ya gabata bayan da majalisar dokokin kasar ta sallami Castillo daga mukaminsa tare da tsare shi saboda yunkurin rusa majalisar a kokarinsa na dakile yankurin tsige shi.

Masu zanga-zangar, da yawa daga cikinsu magoya bayan Castillo, sun kwashe kwanaki suna neman Peru ta gudanar da zabe maimakon barin Boluarte ta ci gaba da mulki har sai wa'adin Castillo ya kare a shekarar 2026.

A waje daya kuma, sabuwar shugaban  da aka rantsar din, Dina Boluarte  ta sanar da cewa za ta gudaanar da zaben kasar kafin cikar wa’adin mulkin da ta karba, bayan da ta ayyana dokar ta baci yankunan da aka yi zanga zangar.

Cikin gaggawa aka rantsar da Boluarte, wadda tsohuwar mai gabatar da kara ce, kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiyar Castillo biyo bayan tsige shi da majalisar dokokin kasar ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.