Isa ga babban shafi
Peru

Majalisar kasar Peru ta haramtawa tsohon Shugaban kasar shiga siyasa

Majalisar kasar Peru a wani zaman ta na jiya juma’a ta sanar da daukar mataki na haramtawa tsohon Shugaban kasar Martin Vizcarra  shiga ko tsoma bakin sa  a duk wani zance da ya shafi tafiyar da ayyukan jama’a ko siyasar kasar tsawon shekaru 10 .

Wasu daga cikin magugunan da aka yi amfani da su a kasar Peru
Wasu daga cikin magugunan da aka yi amfani da su a kasar Peru REUTERS - SEBASTIAN CASTANEDA
Talla

Wani bincike ya tabbatar da hannun tsohon Shugaban kasar a zantukan da suka jibanci rashawa da karkata asu kudade da suka shafi sashen kiwon lafiya,rahotanni daga majalisar na nuni cewa an shi da hannu a zantukan rub da ciki da suka shafi alluran yaki da cutar Covid 19.

Wasu daga cikin magoya bayayan Tsohon Shugaban kasar Vizcara
Wasu daga cikin magoya bayayan Tsohon Shugaban kasar Vizcara AP Photo/Rodrigo Abd

Yan Majalisun sun share kusan sa’o’I  biyar suna tafka muhawara inda ga baki dayan su 86 suka kada kuri’ar amincewa da wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.