Yan ta’adda sun saki wasu ‘Yan kasar China guda biyu a Sahel
Rahotanni daga Burkina Faso sun ce Yan ta’adda sun saki wasu ‘Yan kasar China guda biyu dake aikin hakar ma’adinai bayan kwashe watanni 9 da garkuwa da su.
Wallafawa ranar:
Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa sakin mutanen biyu wadanda aka sace a Nijar.
Jakadan China a Yammai Jiang Feng ya yabawa gwamnatin Nijar akan rawar da ta taka wajen ganin an saki mutanen, inda ya bayyana matakin a matsayin nasarar da hukumomin Nijar ke samu wajen yaki da ta’addanci.
Feng ya bayyana haka ne bayan ganawar da yayi da shugaban kasa Bazoum Mohammed.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu