Isa ga babban shafi
Duniya

Gwamnati ta shiga tattaunawa da manoma a Peru

Gwamnatin kasar Peru a jiya juma’a ta shiga tattaunawa da wakilan manoman kasar biyo bayan zanga-zangar neman karin kudadden da hukumomin kasar ke warewa ga bangaren noma a Peru.

Wasu daga cikin masu goyan bayan zanga-zangar Manoman kasar Peru
Wasu daga cikin masu goyan bayan zanga-zangar Manoman kasar Peru REUTERS/Guadalupe Pardo
Talla

A zaman taron Ministocin kasar na jiya juma’a,gwamnati ta sanar da samar da  wani kwamiti da ya soma aiki a yankin Trujillo,birni dake yankin arewa maso yammacin kasar ta Peru dake da nisan kilometa 500 da babban birnin kasar Lima.

An dai share kusan sa’o’I 7 Ministan ayukan kasar na tattaunawa da wakilan manoman kasar da suka bijire tareda neman a biya musu bukatun su nan take.

Ministan Javier Palacios ya sheidawa manema labarai cewa za su ci gaba da tattaunawa da wakilan manoman a karshen wannan makon don kawo gyara ga wannan ayar doka dake hana ruwa gudu a sashen noma a kasar ta Peru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.