Isa ga babban shafi
Peru

Kuczynski ya lashe zaben Peru

Tsohon ma’aikacin bankin duniya Pedro Pablo Kuczynski ya samu nasara a zaben shugaban kasar Peru bayan da aka kammala kirga akasarin kuri’un da aka jefa a zagaye na biyu zaben a cikin daren da ya gabata.

Pedro Pablo Kuczynski da ya samu nasara a zaben Peru
Pedro Pablo Kuczynski da ya samu nasara a zaben Peru REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Pedro ya yi nasara ne da kyar inda ya samu kashi 50 da digo 12 cikin 100 a gaban abokiyar hamayyarsa Keiko Fujimori wadda ta samu sama da kashi 49 cikin 100 na kuri’un.

Wannan zaben shi ne mafi zafi da aka gudanar a kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, yayin da Kuczynski mai shekaru 77 ya ce, zai dakata har sai hukumar zaben kasar ta fitar da sakamakon karshe kafin ya tsindima cikin murna gadan-gadan.

Sai dai duk da cewa, Kuczynski na gabanta, har yanzu Fujimori wadda ta kasance ‘ya ga tsohon shugaban kasar, ba ta amince da shan kayi ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.