Isa ga babban shafi
Peru

Barack Obama ya samu isowa kasar Peru

A rangadin ban kwana da Shugaban Amurka Barack Obama ya kaddamar ,ya samu isowa kasar Peru a daren jiya juma’a, Obama zai yi amfani da wannan dama domin halartar taron tattalin arzikin kasashen yankin Asia da Pacific dake gudana a Peru.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama Clemens BILAN / AFP
Talla

Obama zai yi amfani da wannan dama domin ganawa da wasu Shugabanin kasashe irinsu China tareda sake duba wasu batutuwa da suka shafi tsaro dama batun kasar Koriya ta Arewa.
Shugaba Obama bayan ganawar sa da Hukumomin Girka, Jamus ya bayyana cewa Amurka ba za ta bada kai yan ta’ada su cigaba kawo rudani ga batun zaman lahiya.
Ranar 20 ga watan Janairu shekarar badi Shugaba Obama zai mika ragamar iko zuwa Donal Trump da ya lashe zaben kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.