Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka ta damu kan rikicin Shi'a a Najeriya

Gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa kan asarar rayukan da aka samu a yayin da jami’an ‘yan sandan Najeriya suka yi arangama da ‘yan Shi’a a jihar Kano.

Kimanin 'yan Shi'a 300 ne aka kashe a arangamar da suka yi da jami'an sojoji a garin Zaria a bara
Kimanin 'yan Shi'a 300 ne aka kashe a arangamar da suka yi da jami'an sojoji a garin Zaria a bara stuntfm.com
Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a wannan jumma’ar ta ce, duk da binciken da ake kan gudanarwa kan lamarin, gwamnatin Amurka ta kadu matuka da martanin da jami’an ‘yan sanda suka yi wa ‘yan Shi’an, abin da ya yi sanadiyar ajalin wasu daga cikinsu.

Amurka ta ce, kungiyar Shi’a na da damar gudanar da ayyuka da kuma bukukuwa na addini a cikin lumana kamar yadda sauran kungiyoyin addinai ke yi.

To sai dai ta bukaci ‘yan Shi’an da su bai wa jami’an ‘yan Sanda hadin kai tare da mutunta doka da oda, yayin da kuma ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta tuhumi wadanda ke da hannu a rikicin da ya hallaka ‘yan Shi’a fiye da 300 a garin Zaria a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.