Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 10 suka mutu a rikicin Shi’a da ‘Yan sanda a Kano

Rikicin da ya auku tsakanin ‘yan sanda da mabiya shi’a ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 10 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Rikicin dai ya auku ne a safiyar yau Litinin, a lokacin da ‘yan shi’ar suka fito domin yin tattaki zuwa garin Zaria kamar yadda suka saba a duk shekara. Wakilin RFI a Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya rawaito cewar ‘yan Shi'ar na ikirarin kashe musu mutane sama da 30.

Jerin gwanon Mabiya Shi'a a Najeriya
Jerin gwanon Mabiya Shi'a a Najeriya stuntfm.com
Talla

01:37

'Yan sanda sun yi arangama da 'Yan Shi'a a Kano

Abubakar Dangambo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.