Isa ga babban shafi
Amurka -Kenya

Shugaban Amurka Barack Obama zai ziyarci Kasar Kenya a yau juma'a

A yau juma'a  ne Barack Obama Shugaban Amurka zai soma ziyara a kasar Kenya, a jiya alhamis shugaban Amurka , ya bayyana fatan da yake da shi wajen ganin cewa, huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Afrika ta dauki wani sabon babi, sakamakon yadda nahiyar ta Afrika ke kan ganiyar farfadowa a cikin hanzari.

Hotunan Shugaban Amurka  a kasar Kenya
Hotunan Shugaban Amurka a kasar Kenya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

A lokacin da ya gabatar da wani jawabi a jiya alhamis a fadar White House a gaban jami’an diplomasiya,yan siyasa da kuma kungiyoyin masu zaman kan su na nahiyar Afrika, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya danganta nahiyar Afrika da zama wani yanki da ci gaban tattalin arzikinsa keda ban mamaki, inda a cewarsa ake samun kasuwanin mafi habbaka a duniya.

Har ila yau shugaba Obama yace a nahiyar Afrika ne ake samun mutane masu ban mamaki dake da hazaka mai ban mamakin gaske.
Saboda haka ne a cewarsa a matsayinsa na shugaba yake aiki tukuru wajen ganin huldar dake tsakanin kasar Amurka da nahiyar Afrika ta cimma wani sabon matsayi mai armashi, inda a nan shugaba Obama ya bayyana kara samun kari yawan hajar kasar Amurka dake shiga nahiyar ta Afrika

Obama ya sanar da kaddamar da wasu ayukan ci gaba da Amurka ta yi a nahiyar Afrika musaman ta fannonin da suka shafi kasuwanci, kiwon lafiya ko kuma tabbatar da samar da wadataciyar cimaka ga nahiyar ta Afrika
Domin tabbatar da abin da ya fada Shugaba Obama yace abin ban sha’awa shine idan aka dauki al’ummar da ta fi kasancewa a cikin farinciki a Duniya da kuma ta yarda da kanta ita ce al’ummar nahiyar Afrika wadanda a kullum suke kan gaba duk da cewa suna fama da talauci da kuma rikece rikice…..
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.