Isa ga babban shafi
Amurka

Obama zai halarci jana'izar bakaken fata a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama a ranar juma’a mai zuwa zai ziyarci garin Charleston na jihar Carolina, inda wani dan bindiga farar fata mai suna Dylaan Roof ya kai hari tare da kashe bakaken fata 9 a wata mujami’a.

Talla

Obama da mataimakinsa Joe Biden za su halarci jana’izar shugaban wannan coci mai suna Clementa Pinckney tare da gabatar da gajeran jawabi a wurin.

Shi kuwa gwmanan jihar Carolina ta kudu inda lamarin ya faru, Nikki Haley, ya bukaci a sauke tutar nan da aka rika amfani da ita a lokacin yakin basasar Amurka kimanin shekaru 150 da suka gabata, wadda ake kallo a matsayin tutar nuna wariyar jinsi tsakanin bakake da farare na kasar, amma yanzu haka take kan ginin Majalisun dokokin kasar.

Tuni dai jami’an tsaro suka kama Dylaan Roof mai shekaru 21 a duniya yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, in da tuhume shi da aikata laifin kisan kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.