Isa ga babban shafi
Iraqi-syria

Sojojin kawance sun kai sabbin hare-hare ta sama a Iraki da Syria

Sojojin kawance a karkashin jagorancin Amurka sun kai hare-hare ta sama har sau 16 a cikin Iraki yayin da suka kai wasu wasu hare-haren har sau 6 a cikin Syria tsakanin jiya juma’a zuwa yau asabar kan mayakan da ke ikirarin jihadi.

Mayakan ISIS a cikin kasar Iraki
Mayakan ISIS a cikin kasar Iraki REUTERS/Thaier Al-Sudani
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar a wannan asabar na cewa a cikin Iraki, an lalala manyan rumbunan ajiye makamai na IS da ke kusa da garin Al Qaim, yayin da aka kange maharan domin hana su motsawa daga inda suke.

Haka zalika an kai wasu hare hare a kusa da garuruwan Mosul, Baiji, Falluja, Makhmur, Ramadi da kuma Sinjar duk a Iraki.

A can kuwa kasar Syria, jiragen yakin sojojin kawancen sun ce sun kai hari kan maboyar ‘yan ta’addan da ke Al Haskah, Ar Raqqah da kuma Tal Abyad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.