Isa ga babban shafi
Amurka-Irak-ISIS

Amruka takara dakaru 450 a kasar Iraki domin ci gaba da yakar kungiyar ISIS

Kasar Amirka na shirin tura Karin Dakarun ta 450 zuwa kasar Iraqi domin shiga yaki da a ke yi da ‘yan kungiyar ISIS dake da'awar kafa daular Islama a yankin gabas ta tsakkiya, sakamakon yadda kungiyar ke ci gaba da samun nasara a Iraki.

Shugaban gwamnatin kasar Iraki Haïdar al-Abadi a lokacin wata ganawa da shugaban Amruka Barack Obama, a 14 avril 2015.
Shugaban gwamnatin kasar Iraki Haïdar al-Abadi a lokacin wata ganawa da shugaban Amruka Barack Obama, a 14 avril 2015. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Tuni dai Shugaban Amirkan Barack Obama ya zartar da tafiyan Dakarun a Iraki, kuma kamar yadda fadar Shugaban ke cewa, ayarin zai shiga cikin Dakarun kasar 3,000 da za a horar ne, da kuma bada shawarwari  tare da duk wani taimako ga Sojan Iraqi, da mayakan sunni domin yaki da ‘yan tawayen Islamar.

Nasarar da kungiyar Isis ke samu a kasashen Iraqi da Syria, bisa dukkan alamu bata yi wa Shugaban Amirkan dadi ba, ganin Amirka ta zaci abinda zata yi kawai shine yakar kungiyar IS ta jiragen sama, a yayinda su kuma sojan kasar su bi ta kasa.

Gwamnatin Amirkan ta kuma amince ta bada  kayan yaki ga Dakarun Irak,i ba kamar yadda lamarin yake ba, inda Gwamnatin Iraki ce, ke gudanar da komai .

Yanzu haka dai mayakan Islama ‘yan sunni basu shiga yaki da ‘yan kungiyar ta ISIS ba, domin sake kwato wuraren da suka kama.

Yanzu da Amirka ke kara yawan Dakarunta a Iraqi, yawan sansanonin horas da Dakaru zai karu daga 4 da ake dasu yanzu haka a kasar.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.