Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Iraqi ta yi fatali da zargin da Amurka ke yi mata akan ISIL

Hukumomin Iraqi sun sa kafa sun yi fatali da zargin da Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ya yi, na cewa jami’an tsaron kasar suna kaucewa fada da mayakan kungiyar ISIL.Carter ya ce bai kamata mayakan masu ikirarin kafa daular Islama su sami nasarar da suka samu a kwanakin nan ba, kan dakarun kasar.

Minista tsaron Iraqi Khaled al-Obeidi da takwaransa na Iran Hossein Dehghan da kuma na Baghdad.
Minista tsaron Iraqi Khaled al-Obeidi da takwaransa na Iran Hossein Dehghan da kuma na Baghdad. Reuters/路透社
Talla

Dama hukumomin birnin Washigton suna gaba-gaba a jerin kasashen da ke taimaka wa Iraqi a kokarin da take yi, na kwato yankunan da mayakan na ISIL suka karbe tun a bara, kuma Firiya minista Haider al-Abadi ya bayyana mamaki da kalaman na Carter.

Shima wani babban jami’in sojan kasar Iran, da ke taimakawa a yakin da ake yi da mayakan na ISIL, ya caccaki Amurka kan kalaman, inda ya ce hukumomin na birnin Washigton sun gagara taimaka wa dakarun Iraqi a birnin Ramadi, duk da kasasncewar sojan kasar a sansanin sojan Al-Asad, da ke lardin.

A halin da ake ciki kuma, mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya fara kokarin kawo karshen cece-kucen da ake yi kan lamarin, inda ya gana da Firiya ministan Iraqi Haider al-Abadi ta wayar tarho.

Fadar White House ta ce Biden na sane da kokari da kwazon dakarun Iraqi, cikin watanni 18 da suka shafe suna arangama da mayakan IS a birnin Ramadi da na sauran wurare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.