Isa ga babban shafi
SYRIA, TURKIYA

Kurdawa na samun nasara a kan mayakan ISIS a Syria

Dubban yan gudun hijira na ci gaba da tserewa fadan da ake tabkawa tsakanin Kurdawa da mayakan  Jihadin kungiyar Isis a kasar Syriya al'amarin da ya haifar da kwararar 'yan gudun hijira a kasar Turkiya.

Dakarun Kurdawa na murnar samun nasara kan mayakan Isis
Dakarun Kurdawa na murnar samun nasara kan mayakan Isis 照片来源:路透社REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Yanzu haka mayakan Kuradawa a kasar Syriya na ci gaba da dannawa zuwa garin Tal Abyad dake rike ga hannu mayakan jihadin islamar kungiyar Isis a kasar Syriya, al’amarin da ya haifar da kwararar yan gudun hijira a kasar Turkiya mai makwabtaka da yankin.

Tuni dai shugaban kasar ta Turkiya Recep Tayyip Erdogan a yau lahadi ya bayyana damuwarsa dangane da kwararar yan gudun hijirar a cikin kasarsa, sakamakon farmakin da mayakan kurdawan ke kaiwa, al’amarin da yace babbar baraza na ce ga kasarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.