Isa ga babban shafi
Amurka

Kotun Amurka ta yi watsi da karar da Kamfanin Madoff ya shigar

Kotun kolin Amurka ta yi watsi da karar da ma'ajin kudin kamfanin Madoff ya shigar yana neman a soke hukuncin da wata kotu ta yanke, inda aka bukace shi da biyan masu ajiya a kamfanin kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka milyan dubu hudu.

Ginin kamfanin Madoff
Ginin kamfanin Madoff (Photo : Reuters)
Talla

Tun a shekarar bara ne wata kotu a birnin New York ta ce ba za a bai wa ma’ajin kudin kamfanin na Madoff wadannan kudaden ba da yawansu ya kai dala bilyan 4 bayan kamfanin ya ruguje a watan disambar shekara ta 2008.

Rugujewar kamfanin dai ta biyo bayan gano cewa Madoff ya damfari dimbin abokan huldarsa, lamarin da ya sa aka yankewa shugaban kamfanin dauri a gidan yari na tsawon shekaru 150, shekara daya bayan rufe kamfanin.

Kotu ta ce kamfanin ya yaudari abokan huldarsa kudaden da yawansu ya haura dala bilyan 65, abinda ake kallo a matsayin yaudara mafi muni da ya taba faruwa a wannan karnin.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da wata karar da babban dillalin kamfanin mai suna Irving Picard ya shigar, da kuma wani kamfani mai suna Securities Investor Protection da ke kare hakkokin masu ajiya a kamfanonin da suka ruguje.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.